Yadda Yan Sakai Ke Kashe Mutane Bisa Zargin Satar Akuya

Yadda Yan Sakai Ke Kashe Mutane Bisa Zargin Satar Akuya

Rundunar Yan Sandan Jihar Katsina Sun Kama Wasu Yan Banga Wato Vigilant  Bisa Laifin Kashe Wani bawan Allah Akan Zargin Ya Saci Akuya. 

Da Suke Fira Da Yan Jarida Sun Bayyana Yadda Suka Kama Wanda Suka Kashe Cikin Kasuwa Suka Tafi Da shi Bayan Gari Suka Kasheshi Sannan Suka Jefa Gawar Rijiya. 

A  lokacin Da Mai Magana da yawun Yan Sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah Ke yi masu Tambaya Sun Amsa Ta Kamar Haka. 

"Yazo Cikin Kasuwa Ne Muka Hadu Dashi To Abinda Ya bamu Mamaki Shine Mun Ta6a Kamashi Da Laifin Satar Akuya Muka Kai Shi Wurin yan San Da Sai gashi Munga yafito. 

To Shine Al'umma Suka Sanardamu Har Yanzu Bai Dai na Wannan Halin ba, Shine Muka Kai shi Daji Muka bugeshi Har Ya Mutu"

To Dama Akwai Dokar Da Tace Ku Kashe Wanda Ake Zargi DA Satar Akuya

"babu Domin Wannan Ma Qaddara Ce Ta Kai mu"

To Bayan Kun Kashe Shi Ya Kukayi Da Gawar. 

"Mun Jefata Cikin wata Tsohuwar Rijiya Dake Bayan Gari"

Wannan Al'amari Ya Farune Bayan Gwamnatin Jahar Katsina Ta Hana Ayyukan Yan Sakai Wato Banga.