Yadda Yan Fashin Daji Suka Bindige Baturen Yan Sanda Har Lahira

Yadda Yan Fashin Daji Suka Bindige Baturen Yan Sanda Har Lahira
Yadda Yan Fashin Daji Suka Bindige Baturen Yan Sanda Har Lahira

Yan Bindi Sun Afka Garin Jibiya Dake Jihar Katsina A Tarayyar Nigeria. 

Yan Fashin Dajin Sun Fara Da Harbin Ka Mai Uwa Da Wabi, Wanda daga bisani suka fara Yunqurin Kutsawa cikin Garin Na jibiya. 

Bayan Samun Wannan Rohoton Ne Gamayyar Jami'an Tsaro Cikin Shirin yaki Suka yi yunkurin Tare Su. 

Bayan Dauki Ba dadi Da musayar wuta ne barayin Suka samu Nasarar Harbe Baturen Yan sandan Jibiyar. 

Tareda Raunata Kwamandan Sojojin Yankin Mai Mukamin Col. 

Shi dai Baturen yan sanda Mai mukamin DSP ya fita ne tare Da yaransa domin fuskatar Maharan Wanda kuma anan ne rai yayi Halinshi. 

Bincike ya tabbatar Da cewa harin bai rasa nasaba Da Hakan Zinare Da akeyi ayankin na jibiya.