Yadda Giwa Ta Murkushe Wani Dan Yawon Bude Ido Wanda Nan Take Ya Mutu Har Lahira

Yadda Giwa Ta Murkushe Wani Dan Yawon Bude Ido Wanda Nan Take Ya Mutu Har Lahira

Wata Giwa ta Murkushe wani Dan Saudiyya Dake Yawon Mude Ido A Uganda. 

Dan kasar Saudi Arabia Wanda ke yawon Bude Ido a kasar Uganda Ya mutu ne alokacin Da Wata Gida ta take shi ba tare Da 6ata lokaci ba kuma yace Ga garinku nan. 

Shidai wannan Mutumin Ya gamu Da Ajalinsa Sa ne yayin Da Suke Tafiya Tare Da Abokan Shi A cikin dajin Murchison Falls National Park akan hanyar su ta zuwa birnin Arua.

Wannan Lamari Dai Yafaru ne yayin Da Suka Fita Da motar su domin Su kama Ruwa inda kuma wani garken dabbobi ya tasa su gaba. 

Shidai marigayin yayi Nisane daga inda abokan nashi suke kuma ya kasa Dawowa. 

Hukumomin dake kula Da gandun daji Sun bayyana Faruwar Lamarin Kuma Sun Tabbatar Da cewa za'ayi Bincike kan Lamarin. 

Wannan dai bashi ne karon farko Da Dabbobin daji ke afkama mutane a Uganda. 

Amma hukumomi a ugandar Sunce Suna bincike kan dalilin faruwar hakan tare Da shan Alwashin kawo karshen hakan.