Wasu daga cikin hakkin Aure akan mata da miji (Ma'aurata)

Wasu daga cikin hakkin Aure akan mata da miji (Ma'aurata)

Daya daga cikin matsalan da a kan samu a aure shine rashin sanin hakkin juna a lokacin zamantakewa ma’aurata. Yana da kyau mata da miji su san hakkokin juna a kan kowane daga cikinsu.

A yau za mu bayyana ma ku wasu daga cikin hakkin miji a kan matarsa.

Ga wasu daga cikin hakkokin:

1 – Soyayya ta gaskiya.

2 – Tsare Amana Miji.

3 – Tausasawa miji da wasa da dariya da shi.

4 – Tsare sirrin miji.

5 – Ba za ta fita daga gidansa sai da izininsa.
[13/01, 10:04 am] +234 802 280 9881: 6- Ba za ta yi azumin nafila ba sai da izininsa.

7 – Ta yarda ya sadu da ita duk lokacin da yake bukata, dan Annabi Mai tsira aminci yace duk matar da taki mijinta ya sadu da ita a duk lokacin da yake so, toh Mala’iku zasu ta la’antar taba zasu su daina ba har sai lokacinda ta yarda da shi. (BUKHARI/MUSLIM).

8 – Ta saurari mijinta kuma tayimasa biyayya matukar ba aikin laifiya umurceta dayi ba.

9 – Mace ta nisanci raina abin da mijinta ya bata, domin Annabi Muhammad mai tsira aminci ya ce “Mata zasu shiga wuta ne saboda kafurce wa mazajensu, wato raina alherin miji” (BUKHARI/MUSLIM)

10 – Ka da mace ta cutar da mijinta da magana ko da aiki.

[13/01, 10:04 am] +234 802 280 9881: 11 – Mace tayi ado da kwalliya wa mijinta, saboda Annabi mai tsira da aminci yace “Allah kyakkyawa ne, kuma yana son kyakkyawan abubuwa, (IMAM MUSLIM YA RUWAITO).

12 – Mace ta tsare dukiyar mijinta da na ‘ya’yansa harma da na gidansa, dan Annabi mai tsira da aminci ya ce “Mace mai kiwo ce a gidanta, za’a tambayeta abin da ta kiwata.

13 – Mace tayi gaggawan baiwa mijinta hakuri a duk lokacin data ga yayi fushi, Tace masa, dan  Allah kayi hakuri, ban san abin da na yi zai ba ta ma ka rai ba, ka yafe mi ni dan girman Allah.

14  -Mace ta yiwa mijinta dukkan irin aikin da ake bukata ayishi a gida.

15 – Mace ta kyautata halayenta ga iyalan mijinta.
[13/01, 10:04 am] +234 802 280 9881: 16 – Mace ka da ta yi abokantaka da mugayen kawaye, sai su hallakar da ke baki sani ba.

17 – Mace ta zama mai tausayawa mijinta, kamar yadda uwa take tausayin ‘Danta.

18 – Mace ta zama mai Biyayya ga mijinta.

19 – Mace ta zama Abokiyar rayuwa ga mijinta.

20 – Mace ta kusanci dukkan abinda mijinta ya ke so.

21- Mace ta nisanci dukkan abin da mijinta ya ke ki.