Shin Da Gaske Rahama Sadau Aure Zatayi? Kuma Waye Zata Aura?

Total Page Views: 11521
Shin Da Gaske Rahama Sadau Aure Zatayi? Kuma Waye Zata Aura?
rahama sadau

A wata dama da jarumar kannywood wato Rahama Sadau Ta ba masoyan ta a Shafin na Twitter Wani ya tambayi jarumar akan Shin zata Iya Daina Film idan tayi aure?. 

Jarumar ta maida Martani inda tace Bazata iya daina Yin film ba ko bayan Tayi aure, Ta Kara da cewa akwai mata da dama Wanda Suke Sana'a kuma basu bari ba har bayan auren su.

Wani ya tambayi jarumar shin menene Dalilin Dayasa Batayi Aure Ba? Inda ta bashi amsa da cew LOKACI NE BAIYI BA. 

Wani ya kara tambayar jarumar shi menene Abinda Yafi Bata Mata Rai?  Shine Tace Rashin Tsaro da Yake Damun Arewacin Nigeria dama Kasa Baki Daya.