Ni Matar Manya Ce Nafi Qarfin Yara _Rashida Adamu

Ni Matar Manya Ce Nafi Qarfin Yara _Rashida Adamu

Jaruma Rashida Me Sa'a Tace Ita Ba  Matar Yara Bace Tafi Qarfin Yaro Yace Yana Santa Da Aure

Tsohuwar jaruma a kannywood haka zalika tsohuwar S.A ta gwamnan jihar kano Dr abdullahi Umar ganduje wacce akafi sani da rashida mai sa'a ta fito ta bayyanawa duniya ita matar manyace ba yara ba.

Jarumar ta fadi hakan ne yayin da hirar da tayi da gidan radion freedom radio dake garin kano a daidai lokacin da dan jarida yayi mata tambaya akan wani matashi wato musa rafin kuka wanda ya fito fili ya nuna soyayyarsa ga jarumar kuma yace ya shirya aurenta da gaske.

Musa rafin kuka yace jarumar tana birgeshi tun yana yaro yana kallon fim dinta kuma tun yana yaro yake son aurenta.

Tace munyi tattaunawa dashi yacemin shi masoyina ne tun lokacin bashida damar fitowa ya fadamin kuma ya rasa hanyar da zai isar da sakonsa a gareni.