Nasarar Zaben Edo Nasarar Kwakwasiyya Ce _Rabi'u Musa Kwankwaso

Nasarar Zaben Edo Nasarar Kwakwasiyya Ce _Rabi'u Musa Kwankwaso

Tsohon Sanatan Kano Ta Tsakiya Dr. Rabi'u Kwankwaso Ya Alaqanta Nasarar Da aka samu a zaben edo da cewa kamar nasarar kwankwasiyya ce. 

Sanatan Ya Taya Gwamnan Jihar Edo Wanda Ya Lashe Zaben Jihar Wato Godwin Obaseki murna sannan ya qara da cewa wannan nasara tasuce su yan kwankwasiyya.

Kwankwason Ya bayyana hakan ne Ta bakin Mai magana da yawunsa a kafafen sada zumunci wato Saifullahi Hassan.

Kwankwaso Yace "Ina Mika Sakon taya Murna ga zababben gwamna Godwin obaseki a karo na biyu kuma muna godewa Allah da wannan nasara.

Ya kara da cewa muna kara godewa yan kwankwasiyya reshen jihar Edo Da kuma hausawa mazauna garin na edo