Mutum hudu ne za su iya hayewa gadon Sarautar Zazzau

Total Page Views: 113
Mutum hudu ne za su iya hayewa gadon Sarautar Zazzau

A Yayin da ake zaman makokin marigayi sarkin zazzau alhaji shehu idris hankalin yan nigeria da arewa ya koma kan yadda zaa nada sabon sarkin da zai mayen gurbin marigayi shehu idris.

A ranar lahadi 20/09/2020 Allah yayiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau Rasuwa Dokta Shehu Idris Wanda ya shafe a qalla shekaru 45 yana jan ragamar mulkin zazzau.

Marigayin shine sarki na goma sha takwas 18 a sarautar zazzau wanda yakeda shekaru tamanin da biyar 85 a duniya.

Bayan rasuwar sa ne da kwana biyu hankulan alummar Najeriya  ya karkata ga sabon sarkin da zaa nada a wannan gari mai albarka wato zariyan zazzau.

Wannan sarauta da kamar yadda jama'a suka sani  bisa tsarinta gidaje hudu ne suke iya yinta wato Gidan Mallawa, Gidan Sullubawa, Gidan Katsinawa da Kuma Bare-Bari.

Masanin tarihin masarautar zazzau da kuma tarihin arewa daga jami'ar ahmadu bello wato shu'aibu shehu ya shaidawa yan jarida cewa kowanne gida daga cikinn bangarorin zai turo da dan takarar sa dan fitar da wanda ya cancanta.

Gwamnan jihar kaduna Nasiru el-rufai Shine Wanda yake da alhakin zabar wanda zai maye gurbin marigayin.