Mawaki Kahutu Rara Ya Rabawa Tsofaffin Jaruman Kannywood Makudan Kudade

Mawaki Kahutu Rara Ya Rabawa Tsofaffin Jaruman Kannywood Makudan Kudade Jiya 

A jiya Mawaki dauda Kahutu Rarara ya yi rabon kudade ga jaruman Kannywood da suka manyanta masu fitowa a iyaye cikin finafinai inda ya rabawa kowannen su naira dubu hamsin hamsin cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin mawakin. 

GWASKA KAFIN ALLAH, CHAIRMAN DIN MAWAKAN JAM'IYYAR APC NA KASA, ALH DAUDA ADAMU ABDULLAHI KAHUTU RARARA, YA BAIWA TSOFAFFIN 'YAN WASAN HAUSA KYAUTAR NAIRA 50,000 GA KOWANNE MUTIN DAYA, A BAN GAREN MAZA DUK WANDA YAGA SUNANSA YA NEMI TIJJANI ASASE, DOMIN YA KARBE DUBU HAMSIN DINSA, HAKA ZALIKA A BAN GAREN MATA KUMA DUK WACCE TAGA SUNANTA TANEMI ABUBUKAR BASHIR MAI SHADDA DOMIN TA KARBE DUBU HAMSIN DINTA.

MAZA
1- BASHIR NAYAYA
2- MODA
3- ISAH JA
4- SANI GARBA S.K
5- BABA KARAMI
6- USAINI SALE KOKI
7- BABA HASIN
8- SHEHU HASSAN KANO
9- ASHIRU NA GOMA
10- BABA SOGIJI
11- KAL'UZU JOS
12- BANKAURA

<

MATA
1- HAJARA USMAN
2- LADIDI FAGGE
3- SAFIYA KISHIYA
4- ASMA'U SANI
5- HADIZAN SAIMA
6- MAMA TAMBAYA
7- SAIMA MUHAMMED
8- LADIDI TUBLES
9- FANDI BORNO
10- BABA DUDUWA
11- HAJIYA SADIYA
12- LUBABATU MADAKI 
13- HAJIYA BINTA OLAH, SUNA GODIYA JAMI'AR WAKA,

wannan ba shine karo na farko da mawakin ke gwangwaje yan masana'antar da abin kirki ba wanda ko a kwanankinnan ya bawa jamila na gudu da tinnani asase kywutar motoci banda wasu da dama da ya gwangwaje a baya da fatan Allah ya saka miji da Alkhairi.