Fatima Ali Nuhi Ta Bayyana Sirrin Abunda Ke Tsakanin Ta Da Mawaki Hamisu Breaker

Fatima Ali Nuhi Ta Bayyana Sirrin Abunda Ke Tsakanin Ta Da Mawaki Hamisu Breaker

Idan Har Baku Manta Ba Ansha Rade-Radin Cewar Akwai Alaka Mai Karfi Tsakanin Fatima Diyar Shahararren dan wasan hausa Wato Ali nuhu Da Kuma Mawaki Hamisu Breaker. 

Wannan Labarin Yayi ta Yaduwa Inda Wasu suke fidin son ransu akan Haka, wanda har wasu suke cewa shi mawakin Wato hamisu breaker ya kai kayan Lefen auren Fatima.

Wannan Lamari dai yayi nisa Inda har wasu suke Dora Hotunan Akwatun lefe Suna Cewa Kasan lefen Hamisu breaker ne da Doyar jarumin Ali nuhu Wanda wannan Maganar wasu na cewa gaskiya ne wasu kuma na cewa ba Gaskiya bane. 

Ana cikin haka sai kwatsam Diyar Ali nuhu Wato Fatima Tayi Rubutu a shafin ta na sada zumunta wato "Social Media" Inda take Bayyana Ma Duniya cewa Babu Abinda ke tskanin ta da Mawaki Hamisu Breaker, Babu Soyayya Tsakanin Su Kawai Karyar Mutane ce suke cewa akwai soyayya tsakanin su. 

Ga Dai Abinda Ta Wallafa Nan A Shafin Nata.