Dalilin Da Yasa Wazirin Katsina Yayi Murabus Daga Sarautar Shi....

Dalilin Da Yasa Wazirin Katsina Yayi Murabus Daga Sarautar Shi....

A Safiyyar Yau Laraba Bane Muka Samu Labarin Bullar Wata Takarda Mai Dauke Da Murabus Din Mai Girma Wazirin Katsina Alhaji Sani Abubakar Lugga. 

Kamar Yadda Sakataren Masarautar Wazirin ya Bayyana Wazirin Ya Ajiye Aikin Shi Ne Tare Da Warware Wani Jawabi Da yayi Akan Matsalar Tsaro akan Jihar Katsina. 

Acikin Wata Takarda Mai dauke Da Shafuka Biyu Wazirin Ya Bada Tarihin Sarautar Gidan Su Ta Wazirci Wanda Daga Bisani Yabada Tarihin Yadda Aka Nada Shi Kan Wannnan Sarauta a 2002.

Sannan A karshe Ya Bayyana Murabus Dinshi Daga Sarautar Sannan Ya Nemi Afuwar Mai Martaba Sarki Idan Hakan Ya 6atama Sarki Rai. 

Dalilin Wannan Dambarwa Dake Faruwa A Wannan Masarauta. 

Wazirin Katsina Yaje Wani Taro A Ilorin Inda Yayi Jawabi Sosai Kan Matsalar Tsaro Da Jihar Katsina Ke Fama Da shi. 

Inda Acikin Jawabin Yace Kusan Kananan Hukumomu 7 basu Hannun Gwamanati suna Hannun Yan Ta-da Qayar Baya. 

Sannan Yace Mafiyawan makarantu Kulle Suke A Yankin. 

Masarautar Katsina Ta Aika Mashi Takarda Domin Ya Fito Ya Warware Wannan Jawabai Da yayi. 

Domin Acewar Masarautar wannan Jawaban Ba Gaskiya Bane. 

Saidai Yayin Da ake Dakon Jiran Amsar Wannan Takardar Sai Aka Samu Takardar Murabus Din Basaraken.