Bazamu Iya Cire Rubutun Larabcin Dake Jikin Kudin Nigeria _ Babban Bankin Nigeria CBN


Total Page Views: 66
Bazamu Iya Cire Rubutun Larabcin Dake Jikin Kudin Nigeria _ Babban Bankin Nigeria CBN

Bazamu Iya Cire Rubutun Larabci Na Jikin Kudin Nigeria Ba Cewar Babban Bankin Nigeria CBN.

Babban Bankin Nigeria CBN Ta Nuna Rashin Amincewarta Qarara Wajen Cire Rubutun Ajami Da Yake A Jikin Wasu Daga Cikin Kudaden Da Nigeria Take Amfank Dasu.

Wani Babban Lauya Mazaunin Jihar Legas Wato Malcom Omirhobo Wanda Yakai Wannan Karar Yace Rubutun Larabcin Na Nuni Da Cewa Nigeria Kasar Musulunci Ce Bayan Kuma Ba Haka Abin Yake Ba A Kundin Tsarin Mulkin Kasar Nan.

Lauyan Yace Shi Sam Baisan Ma'anar Abinda Rubutun Yake Nufi Ba Dan Haka Yake So A Cireshi A Mayar Dashi Turanci Ko Kuma Daya Dag Cikin Harsuna Da Muke Dasu A Nigeria Kamar Irin Su Yoruba, Igbo, Hausa Da Sauransu.

Lauyan Yace Hakan Ya Saba Da Sashi Na 10 Da 55 Na Kundin Tsarin Wannan Kasa.

Saidai Babban Banki Ya Caccaki Lauya Malcom Cewar Baza'a Cire Ba Sakamakon Rubutun Bashi Da Wata Alaka Ta Nuna Kabilanci.