Bayan Dauki Ba Dadi Anyi Nasarar Chafke Wasu Yan Fashi A Karamar Hukumar Kafur.

Bayan Dauki Ba Dadi Anyi Nasarar Chafke Wasu Yan Fashi A Karamar Hukumar Kafur.

Inspector Surajo Sabon Birni Yana Cikin Yan Sanda Da Suka Yi Wannan Artabu Sai Dai Shi An Harbe shi A Qafa.

Bayan Samun Rohoton 6ullar Rohoton Wasu Gungun Yan Ta'adda a Kauyen Dayawa Dake A Karamar Hukumar Kafur Ajihar Katsina.

Rundunar Yan Sanda Sun Hada Wani Samame Domin Tarwatsa Aniyar Maharan.

Ga Yadda abin ya Kasance 

Jami'an Tsaro Sun sami Rohoton Zuwan Wani Babban Dan Ta'adda Wanda Aka Dade Ana Nema Mai Suna Abubakar To Shine Suka Shirya Patrol domin kamashi.

Bayan Zuwan Su Mafakar 6arawon Jami'an Tsaro Suka Bude Wani Daki Dake A Rufe Ashe Yana Cikin Dakin.

Ba Tare Da 6ata Lokaci ba suka Kamashi Bayan kamashi Ne Sauran Yan Uwanshi Suka Ankara Suka Fara Harbin Kan Mai Uwa Da Wabi.

Inda Suka Harbi Inspector Surajo Sabon Birni A Qafa,

Sun Harbeshi A Qirji Sai Dai Yana Sanye Da Rigar Tare Harsashi Basuyi Nasarar Fasa Jikin shi ba.

Anyi Nasarar Chafke Wasu Daga Cikin 6arayin Guda Uku Ciki Harda Wanda Akaje Nema Wato Abubakar.