Banida Laifi Ya Kamata ku tausaya min Ba Ku tsine min ba Inji Rahama Sadau

Total Page Views: 13202
Banida Laifi Ya Kamata ku tausaya min Ba Ku tsine min ba Inji Rahama Sadau

A wata Fira Da BBC tayi da Jarumar kannywood Wato Rahama Sadau Akan Hotunan Batsa da ta Wallafa A Shafin ta na Sada Zumunta, Wanda Har hakan Ya jawo Wani yayi batanci ga Manzon Allah (SAW) Ta Shaida Ma BBC cewa Ita bata da Laifi Akan Abunda Ya Faru. 

Rahamar dai ta Fidi hakan ne A Lokacin Da Daya daga Cikin wakilan BBC yanke mata tambaya Inda Take Bashi Amsar Cewa "Nifa Banida Laifi Akan Abunda Ya Faru Kamata Yayi Ku Tausaya Min Ba Ku Rinka Tsine Min Ba"

Ta Kara Da Cewa Kowa Yasan Rahama Tana Dora Hotuna  a Shafuna Ta Na Sada Zumunta To Wannan Da yayi Comment din batanci ga Manzon Allah (SAW)  Ita batasan Hakan ya faru ba, Sakamakon Idan Ta Dora Hotuna Bata Cika duba comments ba.

Hasalima Wadannan Hotunan Ta Dora su ne Cikin Dare inda da Safe Tayi karo da wannan Comments, Take Cewa Tana ganin Wannan Comment da wannan Mutumi Yayi Hankalinta Ya Tashi Matuka Inda Tayi Sauri Taje Ta Goge Hoton Daga Shafin Nata. 

Amma Sai dai Kafin Ta Goge Wasu har sun Riga da Sun dauki Wannan Comments da wannan mutumin yayi.... 

Ga Bidiyon Ta Nan Inda Take Jawabi akan Yadda Abun Ya Faru.